Ibrahim Magu

Ibrahim Magu
Rayuwa
Haihuwa Maiduguri, 27 ga Augusta, 1966 (58 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a Ƴan Sanda
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

Ibrahim Magu (An haifeshi ranar 5 ga watan Mayu 1962) tsohon dan sandan Nijeriya ne, wanda aka ba riƙon kwaryan jagorancin hukumar (EFCC), kungiyar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya,[1] wanda ake zargi da babakere da dukiya da kadarori hukumar, da aka kwato daga hannun gurbatattun ƴan siyasa.[2] An nada

Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC bayan Ibrahim Lamorde, wanda ya rike matsayin har sau biyu kafin shugan kasa na lokacin Muhammadu Buhari ya sauke shi.[3][4] Dukkansu su biyun, Magu da Lamorde sunyi aiki a karkashin Nuhu Ribadu a lokacin da yake jagorancin hukumar anti-graft kuma ana alakantasu da nasarorin da ya samu a wancan lokacin.[5]

Tarihin Rayuwa da aiki

An haifeshi ranar 5 ga watan Mayu 1962, a Maiduguri, Jihar Borno. Ya halarci makarantar Firamare ta Maiuguri (daga 1969 zuwa 1975). Makarantar sakandare ta Waka Biu (daga 1975 zuwa 1980). Sai kuma Jami'ar Ahmadu Bello Zaria daga 1982 zuwa 1986, inda ya kammala karatunsa a sashin B.Sc Accounting.[6]

Manazarta

  1. "After EFCC chairman, Umar na di most senior cop for Nigeria corruption police". BBC News Pidgin. Retrieved 2020-07-11.
  2. "Buhari 'suspends' EFCC chair, Magu". Daily Trust Newspaper. 7 July 2020. Archived from the original on 7 July 2020. Retrieved 7 July 2020.
  3. "Buhari Sacks EFCC Boss, Appoints Magu As Chairman". Channels Television. Retrieved 18 May 2018.
  4. Ogala, Emmanuel. "Updated: Buhari removes EFCC chairman, Ibrahim Lamorde, appoints replacement". Retrieved 18 May 2018.
  5. Nuruddeen, Abdallah; Isiaka, Wakili; Ismail, Mudashir. "EFCC: Why Buhari fired Lamorde". Archived from the original on 18 May 2018. Retrieved 18 May 2018.
  6. Andrella, Tersoo. "New EFCC Chairman appointed by Buhari". Retrieved 18 May 2018.