Houda Ben Daya ( Larabci: هدى بن داية; An haife ta a ranar 21 ga watan Yulin shekarar 1979 a Tunis) 'yar wasan Judoka ce 'yar Tunisiya, wacce ta fafata a rukunin mata na rabin nauyi. [1] Ta samu lambobin yabo guda biyar da suka hada da zinare uku a gasar cin kofin Afirka da tagulla daga gasar Mediterranean ta shekarar 2001 a kasarta ta Tunisiya, kuma ta wakilci kasarta ta Tunisia a ajin kilo 78 a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2004.[2][3]
Ben Daya ta cancanci shiga tawagar Tunisia a matakin rabin nauyi na mata (78) kg) a gasar Olympics ta bazara a 2004 a Athens, ta hanyar yin nasara a fagen judoka da samun gurbin shiga gasar cin kofin Afrika a kasarta Tunis.[4] Ta yi rashin nasara a wasanta na farko da 'yar wasan Brazil Edinanci Silva, wacce ta ci ippon nasara kuma ta buge ta a kan tatami da uchi mata (inner thigh throw) cikin mintuna uku da dakika goma sha takwas.[5][6]
↑"Comportement des Tunisiens : Deux roses au
milieu des épines" [Behavior of the Tunisians: Two
rose among thorns] (in French). Tunisia Today. 14
August 2001. Retrieved 6 December 2014.
↑"Pas de médaille pour le Congo" [No medals
for Congo] (in French). Congo Page. 10 May 2004.
Retrieved 6 December 2014.
↑"Tunisie: Judo - Houda Ben Daya, triple championne
d'Afrique, qualifiée aux JO d'Athènes : l'émulation est
la meilleure motivation pour progresser" [Tunisia:
Judo - Houda Ben Daya, triple African champion,
qualified for the Athens Olympics: emulation is the
best motivation for progress]. La Presse de Tunisie (in
French). AllAfrica.com . 22 June 2004. Retrieved 10
December 2014.
↑"Judo: Women's Half-Heavyweight (78kg/172 lbs)
Round of 16" . Athens 2004. BBC Sport . 15 August
2004. Retrieved 31 January 2013.
↑"Judoca Edinanci Silva vence tunisiana e está nas
quartas-de-final" [Judoka Edinanci Silva wins over
the Tunisian, and moves forward to the quarterfinals]
(in Portuguese). Folha de S. Paulo . 19 August 2004.
Retrieved 10 December 2014.