Hiba Mohammed

Hiba Mohammed
Rayuwa
Haihuwa 18 ga Janairu, 1968 (56 shekaru)
ƙasa Sudan
Karatu
Makaranta Jami'ar Khartoum
Sana'a
Sana'a molecular biologist (en) Fassara da researcher (en) Fassara
Employers Jami'ar Khartoum
Kyaututtuka
Mamba Global Young Academy (en) Fassara

Hiba Salah-Eldin Mohamed ( Larabci: هبة صلاح الدين محمد‎, an haifeta ranar 18 ga watan Janairu, 1968) 'yar Sudan ce masaniyar ilmin kwayoyin halitta ce wacce ke aiki a Jami'ar Khartoum. Ta lashe lambar yabo ta Royal Society Pfizer Award na 2007. [1]

Rayuwar farko da ilimi

Hiba ta karanci ilimin dabbobi a Jami'ar Khartoum, inda ta samu digiri a shekarar 1993 da Masters a shekarar 1998. Ta koma Jami'ar Cambridge Institute for Medical Research (CIMR) don yin digirinta a 2002.[2] Binciken ta a digirinta, " The role of Host Genetics in Susceptibility to Kala-azar in The Sudan", yana ƙarƙashin kulawar Jenefer Blackwell.[3] [4] Ta kasance a CIMR a matsayin abokiyar karatun digiri.[5] [6]

Bincike

An bai wa Hiba lambar yabo ta Wellcome Trust Research Development Award, kuma ta koma Jami'ar Khartoum don zama farfesa a Sashen Nazarin Halittu. Binciken ta ya mayar da hankali kan fahimtar kwayoyin halittar Visceral leishmaniasis. [7][4]

An ba ta lambar yabo ta 2007 Royal Society Pfizer Award saboda binciken da ta yi kan cutar, wanda cizon Sandfly ke yaɗa shi.[8] Babu wani maganin alurar riga kafi ko ingantaccen magani, kuma mutane miliyan 350 na cikin haɗari a duk duniya. [9][10] Hiba wata ɓangare ce ta bikin makon Royal Society Africa a shekarar 2008.[11] A cikin shekarar 2010, an naɗa Hiba a matsayin Fellow of Global Young Academy.

wallafe-wallafen da aka zaɓa

Duba kuma

  • Sultan Hassan
  • Nashwa Isa
  • Mohammed Osman Baloola

Manazarta

  1. "11 Sudanese Scientists You Should Know About" . 500 Words Magazine . Retrieved 1 November 2022.
  2. Otto, Mark; Thornton, Jacob; Bootstrap. " ﻫﺒﺔ ﺻﻼﺡ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻣﺤﻤﺪ " . manhom.com (in Arabic). Retrieved 1 November 2022.
  3. "Unit Of Diseases And Diversity" . www.iend.org . Archived from the original on 10 October 2018. Retrieved 1 June 2018.
  4. 4.0 4.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :0
  5. "Sudan: Hiba Salah-Eldin Mohamed, a researcher determined to eradicate leishmaniasis :: AWE - En" . africawomenexperts.com . Retrieved 1 November 2022.
  6. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named :1
  7. "Hiba Salah-Eldin Mohamed – Arabian Records (1st post : Eid Al Fitr – 01st Shawwal 1439 (AH) / 15th June 2018 ) / (BETA testing – Research – starting April 2020 till date, on-going)" . Retrieved 1 November 2022.
  8. The Royal Society (23 July 2012), Royal Society Pfizer Award 2007 - Hiba Mohamed , retrieved 1 June 2018
  9. "Sudanese scientist wins top award" . Daily Nation . Archived from the original on 29 March 2019. Retrieved 1 June 2018.
  10. The Royal Society (10 December 2013), In Conversation with Dr Hiba Mohamed , retrieved 1 June 2018
  11. The Royal Society (10 December 2013), In Conversation with Dr Hiba Mohamed , retrieved 1 June 2018