Hadiza Isma El-Rufai(An kuma haife ta ne a ranar ashirin da ɗaya 21 ga watan Yuni, a shekara ta alif ɗari tara da sittin 1960) miladiya.(Ac)Yar Najeriya ce, kuma marubuciya, wacca itace uwargidan gwamnan jihar KadunaMalam Nasir El-Rufai. Hadiza ce ta kafa cibiyar nan na Yasmin El-Rufai Foundation (YELF), cibiya dake maida hankali gurin koyar da ilimi ga mata da ƙananan yara, musamman rubutun ƙirƙira da nazari.
Tarihi
An haifi Hadiza Isma El-Rufa'i a cikin birnin Kano, Najeriya, ga mahaifinta Mohammed Musa Isma tare da uwargidansa Amina Iya Isma.[1] Mahaifinta ma'aikacin gwamnati ne.
Hadiza tayi karatun ta na BSc da MSc a fannin gine-gine a shekara ta alif ɗari tara da tamanin da uku (1983) da kuma MBA a shekara ta alif (1992) duk daga Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria, sannan ta sake yin Masters a Rubutun Kirkira (Creative Writing) a shekara ta 2012 daga Jami'ar Bath Spa, United Kingdom.[2]
Daga nan ne, tafara aiki a matsayin malamar jami'an, a sashen koyar da zane-zane (Architecture) a Kaduna Polytechnic, sannan tayi aiki a hukumar wutan lantarki ta ƙasa wato (National Electric Power Authority, NEPA), kafin nan tazama ma'aikaciya mai zaman kanta.
El-Rufa'i najin harsuna uku Hausa, Turanci da Faransanci.
Rayuwar Iyali
A shekara ta alif Ɗari tara da tamanin da biyar (1985), ta auri Malam Nasir Ahmad El-Rufai wanda suka haɗu dashi a shekara ta alif ɗari tara da sabain da shida (1976 ) a makarantar share fage wato (School of Basic Studies), na Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria.[3] Wanda daga baya yazama Ministan Babban Birnin Tarayya a Najeriya, kuma Gwamnan Jihar Kaduna.
Aikin Rubuce-rubuce
A shekara ta ( 2017), Hadiza Isma El-Rufai ta wallafa littafinta ''An Abundance of Scorpions'' (Ouida Books).[4] littafin nobel ne, wanda tasamu ƙwarin-gwiwa daga aikin data taba yi na sakai a wani gidan marayu dake babban birni Abuja, da kuma Son ta na tayi rubutu akan maraya.[5] An gabatar da littafin a Aké Arts and Book Festival na shekarar (2017).[6]
Helon Habila ya bayyana aikin marubuciyar amatsayin, "wani labari mai ratsa zuciya akan rashi da kuma zaburarwa akan karfin mace da jajircewan ta" wato (a turanci "a heartbreaking tale of loss and an uplifting story of a woman's strength and determination").[7][8]
Taimako (Agaji)
Tare da mijinta, El-Rufai suka kafa Yasmin El-Rufai Foundation (YELF) a shekara ta (2013) domin tunawa da yar'su wacce ta rasu a gidan ta dake birnin London a watan Nuwanba na shekara ta ( 2011).[9][10] Cibiyar koyarwar an bude shine a shekara ta (2017)[11][12] da kudurin rainon yara akan kirkire-kirkire, "musamman ya'ya mata, tsakanin shekaru (8) zuwa(19)" da kuma mata masu tasowa, ta hanyar sama masu da "kayayyaki tare da malamai da littafai da zasu bukata dan karin fahimtar karatun su."[13][14]
A matsayin ta na Uwar-gidan Jihar Kaduna, ta cigaba da amfani da ofishinta wurin ayyukan jinƙai da taimakawa marasa karfi,(talakawa) ta bayar da magunguna ga masu ciwon amosanin jini wato sickle cell patients a garin Kaduna da kewaye.[15][16][17]https