Great Beans of China ( Larabci: فول الصين العظيم) ko Fool el Seen El Azeem fim ɗin barkwanci ne na ƙasar Masar, wanda (Sherif Arafa). ya shirya kuma ya bada umarni a shekara ta 2004.[1]
Takaitaccen bayani
Great Beans of China tauraron ɗan wasa Mohamed Henedi a matsayin Mohyee El-Sharkawi: matashi mai karancin maki, ba shi da aiki, kuma ba shi da kwarewa a rayuwa. El-Sharkawi ba shi da laifi a cikin dangi da ke aikata haramun, waɗanda suke kokarin koya masa ya zama kamar su.[2] Ta hanyar yunƙuri da yawa da ba su yi nasara ba, yana yin abokan gaba da ke zuwa bayansa. A yunƙurin ceto shi, danginsa sun tura shi China, don maye gurbin mahaifinsa a gasar dafa abinci ta duniya.