Ezzeldin Muktar Abdurahman

Ezzeldin Muktar Abdurahman
Rayuwa
Haihuwa Misra, 18 Nuwamba, 1957 (67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Jami'ar Alkahira
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami da mataimakin shugaban jami'a

Ezzeldin Muktar masanin kimiyya ne kuma Farfesa a fannin Pharmacognosy da Ci gaban Magunguna. Ya kasance tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Jihar Bauchi .

Rayuwa ta farko da ilimi

An haifi Muktar a ranar 18 ga Nuwamba 1957 a Misira. Ya sami karatun firamare da sakandare a makarantar firamare ta Banha da makarantar sakandare ta Banha bi da bi a Alkahira. Ya sami digiri na farko na Kimiyya ta Magunguna daga Jami'ar Alkahira (1980). Ya sami Msc (1986), Phd (1998) da MBA (1999) a Pharmacognocy daga Jami'ar Ahmadu Bello (ABU). Ya mutu a ranar 23 ga Nuwamba, 2023.

Ayyuka

Ya yi aiki a matsayin Shugaban Sashen da Dean na Kimiyya na Pharmaceutical na Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria . Ya kuma kasance Mataimakin Shugaban Jami'ar Jihar Kaduna .Ya kasance memba na ƙungiyoyi bakwai na ƙwararru a ciki da waje da Najeriya. A halin yanzu shi ne shugaban kungiyar Nigeria Society of Pharmacognocy .

Kyaututtuka

An ba shi lambar yabo ta Kaduna State PSN, lambar yabo ta Merit (1994), lambar yabo ta PANS ABU Merit, da kuma lambar yabo ta Jami'ar Ahmadu Bello (1995).[1]

Littattafai

Ya na da littattafai sama da hamsin [2] wanda ya rubuta kuma ya hada hannu. [3]

Manazarta

  1. "PSN Board of Fellows Holds Dinner, Awards on July 20". Medical World Nigeria. 14 July 2016.
  2. Agunu, Abdulkarim; Abdurahman, E.M. (15 May 2005). "Analgesic activity of the roots and leaves extracts of Calliandra portoricensis". Fitoterapia. 76 (5): 442–445. doi:10.1016/j.fitote.2005.03.008. PMID 15905046. S2CID 7621368.
  3. "Bauchi State University Gadau". www.basug.edu.ng (in Turanci). Retrieved 11 April 2018.