Dolapo Osinbajo, néeSoyode (an haife tane a ranar 16 ga watan Yulin shekaran 1967) Ta kasan ce lauya ce kuma 'yar siyasa a Najeriya. Matar Mataimakin Shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, tun a shekarar 2015 ta kasan ce Uwar gidan mataimakin shugaban ƙasa kuma mace ta biyu a Najeriya.[1]
Kuruciya da aiki
An haifi Dolapo Osinbajo a ranar 15 ga watan Yulin shekarar 1967, kuma ta girma a Ikenne. [2] Ita jika ce ga Obafemi Awolowo, dan siyasan Najeriya kuma mai matsayi a sarautan Yarbawa, [1] da matarsa Hannah Idowu Dideolu Awolowo, ta cibiyar diyar Awolowo Ayodele Soyode (née Awolowo),
Ta auri Yemi Osinbajo, wanda dan uwanta ne na nesa, a ranar 25 ga watan Nuwamban shekarar 1989. Ta kuma zama kwararrar lauya (a kungiyar Lauyoyin Najeriya) a shekarar 1990. [2]
Dolapo Osinbajo ita ce Babbar Darakta a ƙungiyar mata mai suna Women's Helping Hand Initiative, wata gidauniya ce a garin Epe, Lagos, wanda aka kafa a shekara ta 2014, kuma ita ce ta ƙirƙiro ƙungiyar Orderly Society Trust.
Ayyuka a Matsayin Uwargida Na Biyu
A watan Satumbar shekarar 2019 ta shugabanci taron 49th Benue Women in Prayer (BEWIP), a Makurdi. [3] Ta kuma bude gidan yara na Mama Abyol da kuma Cibiyar Binuwai ta Bunkasa Kirare kere kere (BENCEDI). A jawabinta ga matasa a jihar Benuwe, ta gargade su kan yunƙurin kwafar salon rayuwa na yaudarar intanet. [4] Yayin da take zantawa da 'yan matan da suka kammala makaranta a Legas a watan Disambar 2019, ta kiraye su da su kasance masu riƙon amana a abin kwaikwayo ga na kasa da su. [5] Ta kuma nuna halin cin zarafin mata a matsayin cin zarafin daukakin al'umma ne. [6] A tsakiyar watan Disambar 2019, Uwargidan Shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari, ta nada Osinbajo - tare da matan gwamnonin jihohin Najeriya a matsayin zakarun da zasu jagoranci yaki da tarin fuka a Najeriya. [7]
Ayyuka
They Call Me Mama: Daga littafin Under Bridge Diaries. 2014.