Femi David Lasisi Bamigboye (ranar 7 ga watan Disamban 1940[1] – ranar 21 ga watan Satumban 2018) ya kasance kwamandan sojan Najeriya kuma ɗan siyasa a Jihar Kwara daga watan Mayun 1967 zuwa Yulin 1975, bayan ya rabu da tsohon yankin Arewa lokacin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon.[2][3]
David Bamigboye ɗan ƙabilar Igbomina ne.[4] Ƙanensa shine Theophilus Bamigboye, wani shugaban mulkin soja ya zama ɗan siyasa.[5]
A cikin shekarar 1968 ya kafa ma’aikatar ilimi ta jihar Kwara, tare da sashen da zai kula da al’amuran guraben karatu/Busar.[6] A cikin shekarar 1971 ya sanar da shawarar kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kwara State Polytechnic, wacce aka kafa a cikin shekarar 1972.[7] A cikin watan Disamban 1972 ya buɗe sabon harabar asibitin Ola-Olu tare da masauki ga gadaje talatin da biyar.[8]
A cikin shekarar 1977, an ƙwace wasu ƙadarorin da ya mallaka a Ilorin, ba a mayar da shi ba sai bayan shekaru 26 a cikin watan Mayun 2003.[9]
A cikin shekarar 2009, an naɗa ɗansa Femi David Bamigboye mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kwara.[10]
Kyauta
- Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ne ya ba Bamigboye lambar yabo ta jagoranci a ranar 27 ga watan Mayun 2017.
Manazarta