Damilola Adegbite (an haife ta a Oluwadamilola Adegbite; 18 Mayu, 1985) 'yar wasan kwaikwayo ce ta Nijeriya, Tauraruwa, kuma sananna a shirye-shiryen Talabijin.[1] Ta taka rawa a matsayin Thelema Duke a shirin Tinsel, ta kuma fito a matsayin Kemi Williams a fim din Flower girl.[2] Ta lashe kyautar Gwarzuwar Jaruma (Best Actress) a shirin Talabijin a shekara ta 2011 a gasar Nigerian Entertainment Award.[3]
Tarihin Rayuwa
An haifeta a garin Surulere, jihar Legas. Ta halarci makarantar Queens College dake Yaba, Legas sannan ta karanci harkokin kasuwanci (Business Administration) a Jami’ar Bowen da ke Iwo, Jihar Osun. Tinsel shine shirinta na farko a wasan kwaikwayo.[4] Ta kuma bayyana a cikin tallan TV da shirye-shiryen da aka gabatar a talabijin.[5]
Rayuwar mutum
A watan Agusta 2014, Adegbite tayi aure da Chris Attoh, wani dan wasan fim din da ta hadu da shi a fim din Tinsel na opera.[6] A watan Satumba na 2014, ma'auratan sun samu ḱaruwa ɗa namiji Brian.[7] Adegbite da Attoh sun yi aure na sirri a Accra, Ghana a ranar 14 ga Fabrairu, 2015.[8] A watan Satumba na 2017, labari ya bazu cewa auren Adegbite da mijinta Chris Attoh ya lalace. Adegbite ta haifar da yaduwar jita-jitan bayan ta goge sunan Chris Attoh daga jikin sunanta a asusun ta na sada zumunta. Sannan ta dena biy-biyanshi a shafinta na Instagram, ta goge duk hotunan sa daga asusun ta na sada zumunta.[9] Sa’o’i bayan haka, a zantawa da akayi da Chris Attoh ya tabbatar da cewa aurensa da Damilola Adegbite ya mutu.[10][11]
Fim
Fina-finai
- 6 hours to Christmas (2010)
- Flower Girl (2013)
- The missing a (2017) a matsayin Alero
- Heaven's Hell (2015)
- Isoken (2017)
- Banana Island Ghost (2017)
- Bace (2017)
- From Lagos with Love (2018) a matsayin Samantha
- Merry Men: The real Yoruba Demons (2018) a matsayin Dera Chukwu
- Merry Men: The real Yoruba Demons (2019) a matsayin Dera Chukwu
- Coming from Insanity (2019)
- Cross roads Siwoku (2020)[12]
Shirin Talabijan
- Kafin 30 (2015 – present) a matsayin Temilola Coker
- Tinsel (2008–2012) a matsayin Telema Duke[13]
Gidan wasan kwaikwayo
Manazarta
Hanyoyin haɗin waje
- Damilola Adegbite on IMDb