Anne Aasheim (22 Afrilu 1962 - 30 Maris 2016) edita ce ƴar ƙasar Norway.
Farkon rayuwa da Aiki
An haife ta a Porsgrunn kuma ta fara aikin jarida a babban gidan jaridar birnin Varden a ƙarshen 1970s. Ta yi aiki a Dagen da Bergens Arbeiderblad kafin a dauke ta aiki a NRK Hordaland a 1988.[1]
Darekta
Ta yi aiki a matsayin darekta na rikon kwarya a NRK P3 a Trondheim da NRK P2 a Oslo kafin a nada ta a matsayin darektan gidan labarai na Østlandssendingen a 1997. A shekarar 1999 ta yi aiki a matsayin mukaddashin darektan al'adu a kamfanin dillancin labarai, kafin ta zama darektan labarai na kasa da na gundumomi daga 2001 zuwa 2005. Bayan wani lokaci a matsayin babbar editan Dagbladet daga 2006 zuwa 2010, ta yi murabus kuma ta zama sabuwar manajan darakta na Majalisar Arts Norway a 2011.[1]
Iyali
Ta yi aure da mai bincike Mette Tollefsrud, tayi rayuwa a Ila, Oslo.[2]
↑Valle, Viggo; Mølster, Elisabeth Strand; Johansen, John Magne (19 January 2009). "Anne Aasheim" (in Norwegian). Norwegian Broadcasting Corporation. Retrieved 17 February 2014.