Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, (An haife shi a ranar 1 ga watan Janairu a shekara ta alif 1969, a gida mai lamba 39 Unguwar Mazugal, a ƙaramar hukumar Dala, wanda yake jihar Kano, Najeriya.[1][2] Babban Malamin addinin musulunci ne da ke jihar Kano a Najeriya kuma yana gudanar da karatuttukansa a duk fadin ƙasar. Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa shugaban hukumar Hisba ne wanda yake jahar Kano a ƙaramar hukumar Ungogo. Yana bada karatu a gidan rediyo mai taken tambaya mabudin ilimi wanda Alh. Sani kwangila Yakasai ya kan ɗauki nauyin shi.[3][4][5][6][7][8][9]
Farkon Rayuwa da Ilimi
An haifi Malam Aminu Daurawa a ranar (1 ga watan Janairu, a shekara ta alif 1969) ana kiransa da suna Ibrahim ɗan Muhammad ɗan Bilal a gidan Sheikh Ibrahim Muhammad Bilal wanda aka fi sani da Mai Tafsiri da mahaifiyarsa mai suna, Hajiya Sa'adatu Al-Mustapha a gidan Zakara-Mai-Neman-Suna Unguwar Fagge a Jihar Kano.[10] Mahaifinsa malamin addinin musulunci ne kuma yana sana'ar dinki, yakan koyar da maraice (yamma), kuma yana bada tafsirin Alqur'ani mai girma a duk ranar Litinin da Alhamis a Unguwar Fagge kusa da Tashar Kuka, Bayan ya dawo daga shagonsa na dinki. Mahaifiyarsa kuma daga Bachirawa take, da ke ƙaramar hukumar Ungoggo a Jihar Kano.[11]
Ilimi
Saboda ya taso a gidan ilimi, an turashi makaranta da wuri wanda hakan ya bashi daman haddace Al-Qur'ani da kananun shekarunsa, lokacin yana ɗan shekara 14 kacal. Har wayau, Daurawa ya yi karatunsa na zamani wato firamare da sakandare a jihar kano.
Bayan kammala karatunsa na firamare da sakandare, Sheikh Daurawa ya kuma ci gaba da neman ilimi, domin faɗaɗa karatunsa na addini, a wajen wasu manyan mashahuran malamai na Kano.[12][13][14][15][16][17]
Manazarta
↑"Mal.Aminu Ibrahim Daurawa". www.facebook.com. Retrieved 13 May 2021.