Dala ƙaramar hukuma ce mai ɗauke da jama'a da dama a jihar Kano, Najeriya a cikin birnin Kano, wadda aka ƙirƙira a cikin watan Mayun shekarar 1989, daga tsohuwar ƙaramar hukumar Kano. Dala tana can arewa maso yamma na cikin birnin Kano. Hedikwatar Ƙaramar hukumar Dala tana cikin unguwar Gwammaja a cikin birnin Kano. Ita ce ƙaramar hukuma mafi girma a jihar Kano.
Tarihi
Ƙaramar Hukumar Dala tana ɗauke da Tudun Dalla wanda sunan Ƙaramar Hukumar ya samo asali ne daga Sunan "Tudun Dala" kuma ta taɓa zama babban birnin masarautar Kano.[1]
Yanayin yanki
Tana da yanki 19 km2 da yawan jama'a 2 a lissafin ƙidayar shekarar 2006. Dala ita ce ƙaramar hukuma mafi girma a Najeriya.[1]
Daga cikin shahararrun ayyukan tattalin arziki da kasuwanci a Dala su ne rini, ƙira, yin burodin, yin tukunya, noma, kamun kifi, yin takalma da sauran ayyukan kasuwanci.[1]
Siyasa
Ƙaramar hukumar cibiyar siyasa ce yankin ( Hausa ) ma'ana 'Cibiyar Dimokuraɗiyya ta Najeriya'.
Ilimi
Tana Ɗaya daga cikin makarantun haɗin kan Najeriya, Kwalejin ’Yan mata ta Gwamnati ta Dala.
Mutane
Ƙaramar hukuma ce fitaccen ɗan siyasar nan Malam Aminu Kano wanda haifaffen ƙaramar hukumar Sudawa Gwale ne, amma yana da gidansa na ƙashin kansa a ƙaramar Hukumar Dala, gidan nasa ne gwamnatin tarayya ta mayar da shi cibiyar bincike da horas da dimokaradiyya domin girmamawa gareshi da kuma dawwamar da sunansa, adana koyarwarsa da ra'ayoyinsa ga al'ummai masu zuwa.
Wani fitaccen ɗan kasuwa kuma hamshaƙin attajirin nan na Najeriya, Alhaji Aminu Dantata wanda zuriyarsa suka yi hijira daga Bebeji zuwa Sarari/Koki a ƙaramar hukumar Dala.
Sanannen dangi
Madinawa mafi yawanci ana samun su a Bakin Ruwa.
Manazarta
↑ 1.01.11.2Nigeria, US Embassy. "Amb Campbell's
Speech" (PDF). SPEECH OF THE LOCAL
GOVERNMENT CHAIRMAN CARETAKER COMMITTEE
(ALHAJI MAHMUD SANI MADAKIN) DURING THE VISIT
OF THE AMERICA AMBASSADOR TO NIGERIA AT
G.G.C. DALA ON SATURDAY 2ND JUNE, 2007. US
Embassy Nigeria. Archived from the original (PDF)
on 27 May 2010. Retrieved 10 May 2016.
↑"Post Offices- with map of LGA" . NIPOST.
Archived from the original on 7 October 2009.
Retrieved 20 October 2009.