Khalifa Ahmed Zanna (5 Janairu 1955 – 16 ga Mayu 2015) ɗan siyasan Najeriya ne wanda aka zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya, a jihar Borno, a ranar 9 ga Afrilu, 2011 a zaben kasa yana da shekaru 55. An zabe shi a karkashin jam’iyyar People Democratic Party (Nigeria) kuma aka sake zabe shi a shekarar 2015 kuma ya rasu a ranar 16 ga Mayu, 2015 ‘yan kwanaki kafin rantsar da shi.[1]
Farkon Rayuwa
Zanna ya kasance hamshakin dan kasuwa, kuma memba a hukumar gudanarwar hukumomin tarayya da dama. Misali, a shekarar 2000 yana cikin hukumar kula da wutar lantarki ta kasa NEPA. A shekarar 2007, Zanna na daya daga cikin wadanda suka shirya kungiyar Democratic Women Forum, kungiyar da ke goyon bayan muradun siyasar tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida . Ya kuma kasance mamba a kwamitin gyara bangaren wutar lantarki. An bayyana shi a matsayin dattijo mai kyakkyawan tarihi da hidimartawa jama’a. [2]
Siyasa
Zaben majalisar dattawa
A zaben fidda gwani na PDP, Zanna ya doke tsohon sakataren gwamnatin jihar, Dr Bukar Abba. Ana tunanin Zanna bazaiyi wani tasiri ba a babban zabe, idan aka kwatanta shi da abokin hamayyarsa a takarar Sanata, Gwamna Ali Modu Sheriff . Sai dai cikin sauki Zanna ya doke Sheriff, wanda ke takara a jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP). Zanna ya samu kuri’u 189,232 yayin da Sheriff ya samu kuri’u 120,377, yayin da Alhaji El-Nur Dongel na jam’iyyar CPC ya zo na uku da kuri’u 20,414.
Kaye
Ta yiwu Sheriff ya sha kaye ne saboda rashin gamsuwa da shugabancin sa a tsawon shekaru takwas da yayi yana gwamna. A lokacin mulkinsa tarzoma dama inda aka lalata majami'u da masallatai dama, kashe-kashe da barnata dukiyoyi daga kungiyar Boko Haram, ko kadan ko babu diyya ga kashi 40% na al'ummar jihar wadanda Kirista ne. Bayan kammala zaben, jam’iyyun ANPP da CPC sun yi kira ga Attahiru Jega, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), da ya soke zaben. Sun yi ikirarin cewa sakamakon zabe ya lalace ta hanyar magudin zabe, kisa, tsoratarwa, cusa akwatunan zabe da cin zarafin masu zabe.
Bayan zabensa
Bayan zabensa, Zanna ya yi alkawarin ba da goyon baya don aiwatar da aikin sake farfado da tafkin Chadi, wanda zai kai ruwa daga kogin yammacin Kongo zuwa tafkin Chadi. Tafkin dai ya jima yana bushewa, wanda ya shafi rayuwar manoma da masunta miliyan 25 a Najeriya da makwaftan kasashe. Ya rasu a ranar 16 ga Mayu, 2015, yana da shekaru 60.[3]
Manazarta
Samfuri:Nigerian Senators of the 7th National Assembly
- ↑ https://allafrica.com/view/group/main/main/id/00036894.html
- ↑ https://guardian.ng/news/borno-senator-ahmad-zanna-dies-at-60/
- ↑ https://bornostate.gov.ng/team/ahmed-zanna/ Archived 2022-08-08 at the Wayback Machine