Ahmed Adghirni (An haifeshi a 5 ga watan Mayun 1947 -kuma ya mutu 19 ga watan Oktoban 2020) ɗan siyasan Maroko ne, lauya, marubuci, kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam. Shi dan ƙabilar Abzinawa ne. An haifi Adghirni a Aït Ali a garin Sous, Morocco .
Ya kasance ɗan gwagwarmayar siyasa ga Abzinawan Morocco . Ya kasance mai matukar aiki a Majalisar Amazigh ta Duniya, yana shiga cikin "pre-congress" a Saint-Rome-de-Dolan a 1995 da kuma taron farko a Las Palmas a 1997.
Adghirni ya mutu a ranar 19 ga oktoba 2020 a Tiznit, Morocco yana da shekaru 73.