Zulaihat Ibrahim wacce aka fi sani da Zee pretty ta kasance jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato masana'antar kanniwud, fitacciyar jaruma Kuma shahararriya kyakkyawa a cikin yammatan kanniwud, tayi fina finai da dama, tana daya daga cikin wadan da suka iya rawa a masana'antar.tayi aure a shekarar 2023.[1][2]
Farkon rayuwa
Cikakken sunan ta shine zulaihat Ibrahim inkiya Zee Preety, an haife ta a ranar 9 ga watan satumba a shekarar 1997 a garin rudda Karamar hukumar dankuwa Dake jihar kebbi,tayi karatun ta na firamare a garin lagos,tayi sakandiri a kwantagora a jihar Niger,daga Nan ta shiga kwalejin ilimi Dake jihar sakkoto inda tasami NCE, bayan ta kamnala ta fara aikin koyarwa, Bata tsaya Nan ba ta taho jami,'ar Ahmadu bello Dake Zaria ta cigaba da karatun ta,bayan ta gama ne ta fada harkan fim,babanta immigration officer ne a Lagos,daga baya Akai mashi transfer ya dawo Abuja zuwa Niger,daga baya Kuma aka maidashi jihar kano,zee tun tana karama take da burin zama lauya,daga baya ta koma tanaso ta zama jaruma, inda Allah ya cika mata burin ta.ta shiga masana'antar fim a shekarar 2017 da shigar ta fara haskawa ta daukaka da taimakon sarki Ali nuhu da jarumi Adamu zango.[3]
Fina finai
- Makullim Zuciya
- Akushi
- Bakauye
- Zamantakewa
- Dace da masoyi
- inda so da kaunah
- Sagegeduwa.
Manazarta