An gudanar da Zaben gomnatin tarayya na Kanada na 1957 a ranar 10 ga Yuni, na shekarar 1957, don zaɓar mambobi 265 na majalisar wakilai na Kanada dana majalisar dokokin Kanada ta 23. A daya daga cikin manyan rikice-rikice da akayi a tarihin siyasar Kanada, Jam'iyyar Conservative Party (wanda aka fi sani da "PCs" ko "Tories"), karkashin jagorancin John Diefenbaker, a wannan lokaci ne a kawo karshen waadin mulkin su na shekaru 22 dasukayi na mulkin Liberal, yayin da Tories sukayi nasarar lashe zabe dakuma samun damar kafa Gwamnatin 'yan tsiraru duk da rasa dunbin kuri'un da aka kada ga' yan Liberals.
Jam'iyyar Liberal ta mulaki Kanada tun 1935, inda ta lashe zabe biyar a jere. A karkashin manyan ministoci Ministoci William Lyon Mackenzie King da Louis St. Laurent, kuma ahankali suka gina gomnati sannan suka samar da dukkan nouoi na jindadi da walwalar ar ummagwamnati. A lokacin wa'adin mulkin Liberal na biyar a ofishinsa, jam'iyyun adawa sun zarge su a matsayin masu girman kai da rashin biyan bukatun 'yan Kanada. Abubuwan da suka faru na rikice-rikice, kamar su "bututun muhawara" na 1956 game da gina Trans-Canada Pipeline, sun cutar da gwamnati. St. Laurent, wanda ake kira "kawu Louis", ya kasance sananne, amma baicika kulawa da ministocinsa ba.
Manazarta
"Voter Turnout at Federal Elections and Referendums". Elections Canada. Retrieved March 10, 2019.