A ranar 26 ga Afrilu, 2011 ne aka gudanar da zaben gwamnan jihar Kano a shekarar 2011. Dan takarar PDP Rabiu musa Kwankwaso ne ya lashe zaben inda ya doke Dan takarar jam'iyyar ANPP Salihu Sagir Takai da wasu 'yan takara 12. [1]
Rabiu musa Kwankwaso ya zama dan takarar jam’iyyar PDP a zaben fidda gwani, inda ya samu kuri’u 1,555 inda ya doke Habibu Idris Shuaibu wanda ya samu kuri’u 89, Mohammed Adamu Bello mai kuri’u 71 da Kabiru Kama Kasa wanda ya samu kuri’u 0. [2]
Magaji Abdullahi ya kasance dan takarar ACN, Lawal Jafaru Isa dan takarar CPC . Salihu Sagir Takai ya kasance dan takarar jam'iyyar ANPP .
Sakamakon Zaben
Rabiu musa Kwankwaso daga jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben inda ya doke sauran 'yan takarar 13.[3][4][5][6]
Adadin wadanda sukayi rijistar katin zabe a jahar 5,190,382 Adadin wadanda suka kada kuri'a 2,477,112 Adadin karbarbiyar kuri'a Adadin kuri'ar da aka soke 67,420.
- Rabiu Kwankwaso, ( PDP ) – 1,108,345
- Salihu Sagir Takai, ANPP – 1,048,317
- Lawal Jafaru Isa, CPC - 175,143
- Magaji Abdullahi, ACN – 54,015
- Wasu - 23,872
Manazarta