Yankin Lacs tsohon yanki ne na kasar Ivory Coast. Daga 1997 zuwa 2011, yankin ya kasance yankin na matakin farko na kasar. Babban birnin yankin shine Yamoussoukro sannan yana da fadin 8,875 km². [1] Tun daga 2011, wurin da ya mamaye yankin shi shine Gundumar Yamoussoukro mai cin gashin kanta da kuma wani yanki na Gundumar Lacs. [2]
Bangaren gudanarwa
A lokacin rushewar ta, an rarraba yankin Lacs zuwa sassa biyar: Attiégouakro, Didiévi, Tiébissou, Toumodi, da kuma Yamoussoukro. An kirkiro Sashen Attiégouakro a cikin shekara ta 2009 don haka ya kasance wani sashe na Yankin Lacs na ɗan lokaci kaɗan.
Rushewa
An rushe yankin Lacs a cikin wani ɓangare na sake tsara tsarin gudanarwa na shekara ta 2011 na yankunan na Ivory Coast. Yankunan sassan Didiévi, Tiébissou, da Toumodi sun zama yanki na biyu na Bélier a karkashin sabon gundumar Lacs. Yankin sauran sassan, Attiégouakro da Yamoussoukro, sun zamo cikin sabon gundumar Yamoussoukro mai cin gashin kansa.
Manazarta
6°50′N 5°10′W / 6.833°N 5.167°W / 6.833; -5.167Page Module:Coordinates/styles.css has no content.6°50′N 5°10′W / 6.833°N 5.167°W / 6.833; -5.167Samfuri:Regions of Ivory Coast (pre-2011)Samfuri:Communes of the Lacs Region