Dambun nama nau’in sarrafa nama da ake yi a Arewacin Nijeriya. Ana iya yin dambun nama da kalolin nama kamarsu: naman rago, naman akuya ko kuma naman kaza da sauran dangogin nama. Ana ajiye dambun nama domin tarairayar mai gida, ko kuma saukar baƙi na musamman.
Abubuwan Da Ake Buƙata
1. Nama
2. Kayan ƙamshi
3. Kori
4. Thyme
5. Sinadarin ɗanɗano
6. Yaji haɗaɗɗe
7. Albasa da tafarnuwa
Yadda Ake Haɗawa
1. Da farko za a sami nama, a yanke wajen da babu kitse sai a wanke nama ya fita tas.
2. A cikin tukunya babba a zuba wannan nama da wadataccen ruwa, sai a zuba su albasa, kayan ƙamshi, kori, thyme da ɗan sinadarin ɗanɗano.
3. A bar naman ya dahu sosai, har sai naman ya fara dagargajewa….in ruwa ya kusa ƙarewa sai a ƙara ruwa domin ya isa dafa naman.
4. Cikin turmi mai tsafta a zuba nama a daka har sai ya daku.
Daga Hafsat_Shettimah: Wasu daga wannan gaɓar suke zuba mai a cikin tukunya, su yi ta juyawa, har sai naman ya soyu amma ni ga yadda nake nawa.
5. A zuba wadataccen mai cikin tukunya mai zurfi, sai a zuba wannan dakakken nama, a yi ta juyawa da muciya, har sai nama ya fara yin ja, sai a ɗebo wannan yaji a zuba. A nan za a sake jin ƙamshin ya tashi sosai.
6. A wannan lokaci naman ya kusa sauka, sai a kula da wajen juyawa domin kar nama ya soyu da yawa ko ya ƙone. A kula wurin juyin, domin in an bar shi zai ƙone.
7. A sami kalanda mai kyau, da tukunya sai a juye sai a bar shi har sai man jiki ya tsane tas da kansa [1]