Wilson Edgar Pereira Alegre (an haife shi a ranar 22 ga watan Yuli a shekarar 1984 a Huambo) shi ne mai tsaron ragar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Angola wanda a halin yanzu yake taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Libolo.[1]
Sana'a
Wilson ya buga wa Recreativo Caála wasa tun a shekarar 2008, kuma tun daga lokacin ya kasance lamba 1.[2]
Ayyukan kasa da kasa
Har ila yau Wilson ya samu buga wa tawagar kwallon kafar Angola wasa a farkon shekarar 2010 a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2010.[3]
An kuma saka shi a gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2010 tare da wasu masu tsaron gida Lamá da Carlos.[4]
Manazarta
- ↑ Girabola. "Página Não Encontrada | Girabola" .
www.girabola.com (in European Portuguese).
Retrieved 2017-07-27.
- ↑ Wilson at Footballdatabase
- ↑ "Wilson" . National-Football-Teams.com .
- ↑ Wilson Alegre Sports Reference LLC. Archived from the original on 18 April 2020. Retrieved 13 August 2017.