Waziri Muhammad Saleem ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba a Majalisar Gilgit Baltistan tun Nuwamban shekarar 2020.
Siyasa
Saleem ya tsaya takarar Majalisar Gilgit-Baltistan a zaɓen 2020 a ranar 15 ga watan Nuwamban 2020 daga GBA-9 (Skardu-III) a matsayin ɗan takara mai zaman kansa. Ya lashe zaɓen ne da tazarar kuri’u 1,099 a kan ‘yar takara Fida Muhammad Nashad ta Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI). Ya samu ƙuri'u 6,286 yayin da Nashad ta samu kuri'u 5,187. Bayan ya lashe zaɓe Saleem ya koma PTI.[1][2]