The Hunger (Al-Go'a, الجوع)[1] fim ne na wasan kwaikwayo/soyayya na ƙasar Masar da aka shirya shi a shekara ta 1986, tare da Souad Hosni, Yousra da Mahmoud Abdel Aziz.[2]
Labarin fim
Fim din, wanda ya samo asali ne daga littafin Naguib Mahfouz mai suna iri ɗaya, yana bincika yanayin zamantakewar Cairenes a farkon shekaru goma na karni na ashirin. A yin haka, duka fim ɗin da littafin suna magana sosai game da jigogi na talauci da mutuwa.[3]