Sheikh Ahmad Abulfathi Alyarwawee |
---|
Sheikh Ahmad Abulfathi (RTA) Babban malami ne wanda ya koyar kuma yayi umurni da a koyar da addinin islama,ta hanyar sufaye. Shehi (Murshid) ne na darikar Tijjaniya wanda kuma ya rayu a ƙasashen; Nijeriya, Nijar, Cadi da kuma Senegal tsakanin shekarar alif 1919 da shekara ta 2003 miladiya. Shi mutumin Konduga ne a Jihar Borno, kasar Nijeriya.
Nasabar sa
Shine Ahmad bin Aliyu bin Ahmad bin Aliyu bin Mustapha bin Mukhtar bin Adam bin
Dawud bin Abdulganiyyu bin Zubair bin Abbas bin Hussain bin Suleiman bin Ishaq (ta kan wannan suka hada kaka daya da SHEHU TIJJANI) bin Aliyu Zainul Abidin bin Ahmad bin Muhammad Nafsuz-zakiyya bin Abdullahil kamil bin hasanul-musanna Bin Hassanul Sibɗiy bin Aliyu bin Abiy Ɗalib wa Faɗimah Bintu Muhammad SAW.
Tsakanin Shehu Abulfathi da Imam Aliy, akwai mutane goma sha tara, Alhamdulillah.
Littafin da ya Wallafa
Ya wallafa litattafai mai yawa, a cikin su akwai:
- Ifadatul Kiram Fi’tarih Maulid Khairul Anam
- Al’ajiwiba Ahmadiyya Li masa’il Duniya Wa Tariqa Ahmadiiyya Tijaniyya
- Al’ajiwiba Ahmadiyya Fi Mas’ala Ibrahamiyya
- Alqatamas Fi sharhi suratul Ikhlas
- Tuhfatul Adfal Fi Nahwu
- Takrib Qawa’id Irab Limubta’idina Minal Dulab
- Jawahir Rasa’il
- Hilasatu Jawhar Fi Qawa’id ilmi Ma’ani Wal Bayan
- Rihilatu Ahmad Yarwa Li talbiyati Da’awatu Turk Sufiyah Fi Biladi Maghribiyah
- Risalatu Faydha Rabaniya Fi Taqyid Shrud Tariqa Tijaniyya
- Risatu Fi Sujud Sahwu
- Rihilatu Barriya Wa Bahriya Liziyarutu Sahibil Asar
- Ziyadatu jawahir
- Shaddu Rihal Fi Hajj Wa Umrah
- Sharhu Jawharatu Kamal
- Fathu Al’ali Kareem Fi Salati Ala Nabiyul Azeem
- Kanzul Rashad Fi Wa’azu Wal Irshad
- Mu’ayin Dalib Alragib Fi Ma’arifatu Mustala’a Hadith
- Nata’ij Al-asfar Fi Salati Ala Sayyidina Muhammad Nabiyil Mukhtar
- Wamdatu Min Durar Sheikh Abulfathi
Wafati/Rasuwa
Shehi yayi wafati a ranar Laraba 21 ga watan Safar 1424 A.H. wanda yayi daidai da 23 ga watan April 2003. Ya bar matan aure hudu da yaya arba'in da shida (46), ya'yan sa duka hamsin da uku ne (53) amma bakwai sun rasu tun Shehi yana raye, daga cikin su akwai Sayyadi Barhama wanda aka yi masa rauda a damaturu, Allah ya kara musu yarda.
Manazarta