Sheik (shehu) tana kuma nufin babban malami wanda yake da matukar sani a fannikan ilimi daban-daban
Ma'anarta a wajen sufaye tana nufin duk mutumin da iliminsa ya kai a yi masa tambayoyi guda dubu kuma yabada amsar su a take. [2]
Ma'anar ta da larabci
Tana nufin mutum wanda yake da yawan shekaru.
Tana nufin mutum wanda yake jagorancin wani addini.
mutum da yake da girma a wata ƙabila
mutum da yake jagorancin wata ƙabila
Tana nufin Mutun mai yawan shekaru musamman ma daga shekara hamsin zuwa shekara tamanin
Anyiwa mutane da yawa lakabi da kalmar shehu a kasar Hausa suna da yawa, wanda suke manyan masana da manyan malamai da manyan mutane a kasar Hausa da wasu sassa na duniya.[3]
Daga cikin na kasar Hausa suna da shehu Usman dan Fodio wanda aka fi sani da mujaddadi, Kuma ana yiwa mafiyan yaron da aka sa masa sunan shehu usman wato Usman da shehu domin girmamawa a gare shi da nuna kimar sunansa da alfarmar da yake da ita wajen musulmai musanman ma mutanen arewacin Najeriya da kuma mutanen Nijer.
↑Abun-Nasr, Jamil M. (2007). Muslim Communities of Grace: The Sufi Brotherhoods in Islamic Religious Life. Columbia University Press. p. 94. 08033994793.ABA.