Sharon Fonn Farfesa ce ta Afirka ta Kudu a fannin Kiwon Lafiyar Jama'a a Jami'ar Witwatersrand. Ayyukanta suna mai da hankali ne kan ciwon daji na mahaifa, tsarin kiwon lafiya da haɓaka ƙarfin Afirka da binciken lafiyar jama'a.
Sana'a da tasiri
Fonn ta yi aiki a matsayin shugabar Jami'ar Witwatersrand Makarantar Kiwon Lafiyar Jama'a daga shekarun 2003 zuwa 2011.[1] Ita memba ce a Kwalejin Kimiyya ta Afirka ta Kudu.[2] Farfesa Fonn ta taimaka wajen kafa bincike mafi daɗewa a Afirka game da yara tun daga haihuwa.[3] Ta wallafa muƙaloli a game da kimiyya sama da guda 50. [4]
Kyaututtuka da karramawa
Ta samu digiri na girmamawa a Sahlgrenska Academy.[5]
↑"Members". www.assaf.org.za (in Turanci). Retrieved 2017-12-30.
↑Fonn, S.; de Beer, M.; Kgamphe, S.; McIntyre, J.; Cameron, N.; Padayachee, G. N.; Wagstaff, L.; Zitha, D. (1991-04-20). "'Birth to Ten'--pilot studies to test the feasibility of a birth cohort study investigating the effects of urbanisation in South Africa". South African Medical Journal = Suid-Afrikaanse Tydskrif vir Geneeskunde. 79 (8): 449–454. ISSN0256-9574. PMID2020885.