Samuel Aruwan (an haife shi 10 ga Mayu 1982) ɗan jarida ne, kuma Kwamishinan na farko a Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna daga shekara ta 2019 zuwa 2023. Ya yi kuma Kantoma da Kwamishinan birnin Kaduna daga shekara 2023 zuwa 2024. Yayi aiki kuma matsayin Babban Mai Bada Shawara akan yadda labarai harwa yau kuma mai magana da yawun gwamna daga 2015 zuwa 2019. A yanzu haka kwarare ne a harkan tsaro.
Tarihi
Samuel Aruwan haifaffen gundumar Tudun Wada, dake karamar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna, Najeriya. Shi kwararren ɗan jarida ne wanda yake da ƙwarewa fiye da shekaru goma kafin ya shiga aikin gwamnati a 2015.
Aruwan ya da digiri na biyu a kan jarida da sadarwa daga jami'ar Ahmadu Bello Zariya, bayan kamala karatun jarida da sadarwa a kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kaduna. A shekarar 2012, ya halarci horon horar da 'yan jarida na binciken Afirka a jami'ar Witwatersrand, Afirka ta Kudu. Ya kasance daya daga cikin ‘yan jaridar Najeriya da aka horar kan yadda za a dakile tsattsauran ra’ayin addini a Tony Blair Institute for Global Change, London a 2014 da kuma a Drew University’s Institute on Religion and Conflict Transformation, New Jersey in 2016. Ya kuma halarci Jam'iyar Cranfield da ke Ingila a kan yaki da ta'adanci da kuma kare muhimmar kadarorin kasa, da kuma samo bayanan siri. A yanzu haka dalibi ne a jam'iyar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Manazarta
https://www.channelstv.com/tag/samuel-aruwan/
http://www.citypeopleonline.com/meet-gov-el-rufais-tireless-spokesman/
https://punchng.com/el-rufai-makes-spokesman-security-commissioner/