Samuel A. Ilori

Samuel A. Ilori
Rayuwa
Haihuwa 11 ga Janairu, 1945 (79 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Oxford
Thesis director Aubrey William Ingleton (en) Fassara
Dalibin daktanci Deborah Olayide Ajayi (en) Fassara
Bamidele Ayodeji Oluwade (en) Fassara
Michael O. Ajetunmobi (en) Fassara
Hammed Praise Adeyemo (en) Fassara
Sana'a
Sana'a masanin lissafi
Employers Jami'ar Ibadan
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya

Samuel A. Ilori malami ne dan Najeriya a fannin lissafi a tsangayar lissafi ta Jami'ar Ibadan Najeriya.[1] Ya kasance tsohon shugaban Sashen Lissafi, Shugaban tsangayar lissafi, tsohon Provost na Kwalejin Kimiyya da Fasaha, kuma tsohon Shugaban Kungiyar Lissafi ta Najeriya. Shi ma memba ne na Kwalejin Kimiyya ta Afirka.[2]

Rayuwar farko da ilimi

An haifi Ilori a ranar 11 ga Janairu 1945. Ya sami digiri na farko, B.Sc. a fannin lissafi tare da karramawar ajin farko a shekarar 1968 daga Jami'ar Ibadan dake Najeriya. Daga nan sai ya koma kasar Ingila inda ya sami Diploma a Advanced Mathematics a shekarar 1969 daga Jami’ar Oxford, sannan a shekarar 1972 ya samu digirin digirgir na D.Phil. digiri a fannin lissafi daga jami'a guda.[3]

Aiki

Ya kasance shugaban sashen Physics da Mathematics daga 1977 – 1979. Daga baya, ya ci gaba da zama shugaban tsangayar ilimi a shekarar 1990 da kuma Provost of Science and Technology a 1994. A 2003, ya zama shugaban sashen lissafi.[3]

Manazarta

  1. "SA.ILORI | Faculty of Science, UI". sci.ui.edu.ng. Retrieved 2022-06-29.
  2. "Ilori Samuel A. | The AAS". www.aasciences.africa. Archived from the original on 2019-10-26. Retrieved 2022-06-29.
  3. 3.0 3.1 "Prof. S. A. Ilori – Member - Ajayi Crowther University, Oyo" (in Turanci). 2013-02-20. Retrieved 2022-06-29.