Sallaya ko daddumar sallah wasu kan kira ta tabumar sallah wani dadduma ne ko fallen ƙyalle, wani lokacin ana amfani da kafet, musulmai ke yin amfani da shi da wasu ɓangare na Kiristoci da mabiyan addinin Baha'i dan yin bauta akai.
A musulunci, ana shimfiɗa tabarmar sallah ne a ƙasa dan mai bautar ya hau kai saboda kasancewa cikin tsafta da kuma ake bauta. Wannan ya haɗa da sanda mai yin sallar ke sajuda da zaman tahiya. Musulmi dole sai yayi alwala kafin yayi Sallah, kuma dole ya yi sallah a wuri mai tsafta.