Ruwa ne da ke sauka daga sararin samaniyya wanda Allah, (S.W.T) shine yake saukar da shi a kowane lokaci dare ko ranar[1], wani lokaci mai yawa wani lokaci kuma ya yi kadan. Amma mafi yawan cin lokaci ya fi zuwa da hadari, wanda hausawa suke mashi lakabi, da (Ruwa kaman da bakin kwarya).
Sai kuma yayyafi, shi yayyafi mafi akasari yana zuwa ne a hadarin da bai saukar da ruwa ba, Sai kuma misali lokacin marka-marka shi kuma a wannan lokacin zaka ga ruwa ba dare ba rana,koda yaushe ruwa Kawai akeyi sai dai ya dauke ya kuma dawo. A wani lokaci ruwan yayi karfi wani lokacin kuma baya yin karfi, to wanda bai yi karfin ba shi ne ake kira da yayyafi.[2][3]
.
A Larabci ana kiransa da "مطر".
Hadari
Shi dai hadari shi ne kusan ace ginshikin ruwan sama wanda mafi yawan ruwan saman da ake yi sai hadari ya hadu ya taso yayi iska sannan sai ruwa ya zo, wani lokaci a hade da iska wani lokacin kuma zallan ruwan ne. Menene Hadari ? Hadari dai shi ne haduwar giza-gizai waje daya musamman bakaken giza-gizai sai su dunkule waje daya su tado da iska daga nan bayan iska sai ruwa ya biyo baya, sai dai akwai abunda ke kawowa hadari cikas shi ne bakan gizo wanda zaka ganshi wani ja-ja da yalo-yalo kala dai kusan uku, to idan ya kewaye hadari zaka ga sai dai hadarin nan yayi yayyafi, to wannan yayyafin hausawa na kiran shi "aman bakan gizo".
Marka-Marka
Wani dan tsakaitaccen lokaci ne na damina inda ake yin ruwa akai-akai ba tsakaitawa.