Rikicin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

Western DR Congo clashes

Rikicin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo jerin hare-hare ne da mayakan Mobondo suka kai kan sojoji da fararen hular Teke wanda ya fara a watan Yunin 2022.[1] Rikicin yana da nasaba da kabilanci, domin Mobondo galibi ana daukar su ne daga Yaka da sauran kabilun da ke yin kaura zuwa yankunan da Teke ke zaune.[2]

Tushe

Yankunan arewa maso gabas na Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, musamman Batéké Plateau, a tarihi sun kasance marasa ci gaba da talauci.[3] ’Yan asalin yankin na mutanen Teke ne.[4] A tsawon lokaci, bakin haure 'yan kabilun lardunan da ke makwabtaka da su kamar Kwilu da Kwango sun fara kutsawa cikin yankunan Teke na gargajiya, suna neman filaye don kafa gonaki. Bakin hauren, galibinsu Yaka, Mbala da Suku, an ba su izinin zama da sharadin cewa za su biya harajin gargajiya na sarakunan Teke.

Lokacin Da Ya Fara

Rikicin dai ya faro ne a ranar 9 ga watan Yunin 2022 a kauyen Masia-Mbe, a yankin Bateke Sud na Mai Ndombe, inda manoman Yaka da Mbala suka taru domin nuna adawa da karin haraji. Jama’a sun yi tattaki zuwa gidan wani basarake, suka fara jifa da duwatsu; Dan uwan sarkin ya mayar da martani ta hanyar bude wuta da bindigar farauta tare da kashe wani manomin Yaka daya. A wani mataki na ramuwar gayya, sai washegari manoman Yaka suka dawo da yawa, suka afkawa Masia Mbe, suka kona gidan basaraken tare da wawashe kauye. Tun daga nan ne rikicin filaye da haraji ya zama ruwan dare, inda Kwamouth ta zama cibiyar fada. A karshen watan Yuni, Yaka ya shirya ƙungiyoyi masu dauke da makamai, tare da sunan "Mobondo" bayan layukan kariya.

Manazarta

  1. https://www.thenewhumanitarian.org/news-feature/2024/02/12/conflict-western-drc-democratic-republic-of-the-congo-amid-rebel-gains-east
  2. https://www.africanews.com/2023/05/12/kinshasa-conflict-one-soldier-and-four-militiamen-killed//
  3. https://www.radiookapi.net/2024/07/15/actualite/securite/mai-ndombe-plus-de-50-morts-apres-une-attaque-de-la-milice-mobondo
  4. https://www.hrw.org/news/2023/03/30/dr-congo-rampant-intercommunal-violence-west