Rao Muhammad Ajmal Khan ( Urdu: راو محمد اجمل خان ; an haife shi 20 Agusta 1954) ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba a Majalisar Dokokin Pakistan daga watan Agustan 2018 har zuwa watan Agustan 2023. A baya ya kasance ɗan majalisar tarayya daga shekarar 2002 zuwa shekarar 2007 da kuma daga watan Yunin 2013 zuwa watan Mayun 2018.
A halin yanzu yana aiki a matsayin mataimaki na musamman ga Firayim Minista, tare da matsayin Ministan Jiha [1]
Rayuwar farko
An haife shi a ranar 20 ga watan Agustan 1954.[2]
Harkar siyasa
An zaɓe shi a Majalisar Dokokin Pakistan a matsayin ɗan takara mai zaman kansa daga Mazaɓar NA-146 (Okara-IV) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2002 .[3] Ya samu ƙuri'u 62,711 sannan ya doke Rao Muhammad Safdar Khan, ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (PML-Q).[4]A watan Agustan shekarar 2003, an naɗa shi sakataren harkokin man fetur da albarkatun ƙasa na Majalisar Tarayya.[5]
Ya tsaya takarar kujerar Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin ɗan takarar PML-Q daga Mazaɓar NA-146 (Okara-IV) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2008 amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 46,006 sannan ya sha kaye a hannun Manzoor Wattoo . A wannan zaɓen, ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Punjab a matsayin ɗan takara mai zaman kansa daga Mazaɓar PP-192 (Okara-VIII) amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 65 sannan ya sha kaye a hannun Malik Ali Abbas Khokhar .[6]
An sake zaɓen shi a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin ɗan takarar Pakistan Muslim League (N) (PML-N) daga Mazaɓar NA-146 (Okara-IV) a babban zaben Pakistan na 2013 .[7][8][9][10][11] Ya samu kuri'u 109,998 sannan ya doke Manzoor Wattoo.[12]A lokacin da yake zama dan majalisar tarayya, ya taba zama sakataren majalisar tarayya mai kula da masana’antu da samarwa.[13]
An sake zaɓen shi a Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar NA-143 (Okara-III) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2018 .[14]
Manazarta