Pierre Toura Gaba (a shekarar 1920 – 1998) ɗan siyasan Chadi ne kuma jami'in diflomasiyya. Bayan samun 'yancin kan Chadi, ya zama Ministan Harkokin Wajen ta na farko daga shekarar 1960 zuwa 1961.
Rayuwa da Aiki
An kuma haife shi ne a ranar 28 ga watan Disamban shekarar 1920 a Maibyan, kusa da Moissala, a yankin Moyen-Chari da ke kudancin ƙasar Chadi. Ya yi aiki a matsayin jami'in diflomasiyya a Brazzaville kuma ya yi aiki na dogon lokaci a matsayin malami a wurare irin su Ati, Abéché, Bongor da Fort-Archambault (wanda ake kira Sarh a yanzu).