Oran (lafazi : /oran/ ; da harshen Berber: ⵡⴰⵀⵔⴻⵏ; da Larabci: وهران/Wahran) birni ne, da ke a ƙasar Aljeriya. Shi ne babban birnin yankin Oran. Oran tana da yawan jama'a 609 940, bisa ga jimillar shekarar 2008. A 2010 kuwa adadin kidayar mutane yakai 853,000. An gina birnin Oran a shekara ta 903 bayan haifuwar Annabi Issa.
Oran shine birni nabiyu mafi girma a kasar bayan birnin Aljir ansan birnin da hadahadar kasuwanci.