Old Government Reserved Area ( Old GRA ) unguwa ce a cikin birnin Fatakwal, Jihar Ribas a Najeriya. Turawa mazauna yankin ne suka fara zama a lokacin mulkin mallaka sannan kuma ana kiran sunan anguwar da: yankin turawa.
A matsayin yanki mai hade-haɗe, Old GRA ta haɗa wuraren zama, nishaɗi da ma kasuwanci. Unguwar ta yi iyaka daga gabas da Abuloma, daga arewa kuma iyaka da unguwar D-line, daga yamma da Diobu da tsibirin koda sannan daga kudu da Borokiri.[7] Yankin ya ƙunshi Zip code 500241[8]
Ilimi
Makarantu
Makarantun firamare da sakandare ko wasu cibiyoyin ilimi da ke aiki a cikin iyakokin Old GRA sun haɗa da:
Bereton Montessori Nursery and Primary School, 8 Ernest Ikoli Street