Ningi ƙaramar hukuma ce dake a Jihar Bauchi, a arewa maso gabashin Nijeriya.Tana daga cikin ƙanƙanin hukumomi guda ashirin na jihar. An kafata ne tun bayan juyin juya halin khalifancin sokoto, ƙungiyar masu hawan dutse waɗanda ba musulmi ba, wadanda a tsawon karni na 19 suka nuna matukar turjiya ga fadan ko masarautar Bauchi da na Kano da kuma na Zazzau. Daya daga cikin masu mulkin da suka yaki masarautar Kano shine akafi sani da Gwarsum.
Manazarta
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.