Muhammad Hanif Malik Awan ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya taɓa zama memba na Majalissar Lardin Punjab, daga shekarar ta 1997 zuwa ta 1999 da kuma daga watan Yunin 2013 zuwa watan Mayun 2018. Ya kasance memba a Majalisar Dokokin Pakistan daga watan Disambar 2012 zuwa watan Maris na shekarar ta 2013.
Rayuwar farko da ilimi
An haife shi a ranar 5 ga watan Mayun 1952 a Gujrat .[1]
Ya sami ilimin matakin digiri .[1]
Harkokin siyasa
Ya tsaya takarar kujerar majalisar dokokin lardin Punjab a matsayin ɗan takara mai zaman kansa daga Mazaɓar PP-95 (Gujrat-cum-Jhelum) a babban zaɓen Pakistan na shekarar ta 1993 amma bai yi nasara ba. Ya samu ƙuri'u 20,726 sannan kuma ya sha kaye a hannun ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (PML-J).[2]
An zaɓe shi a Majalissar Lardi ta Punjab a matsayin ɗan takarar Pakistan Muslim League (PML-N) daga Mazaɓar PP-95 (Gujrat-cum-Jhelum) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 1997 . Ya samu ƙuri'u 29,854 sannan ya doke ɗan takarar PML-J.[2]
Ba zai iya tsayawa takara a babban zaɓen shekarar 2002 ba saboda buƙatar kammala karatun digiri.[3]
An zaɓe shi a Majalisar Dokokin Pakistan daga Mazaɓar NA-107 (Gujrat-IV) a matsayin ɗan takarar PML-N a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a shekarar ta 2012.[3][4] Ya samu ƙuri'u 70,434 sannan ya doke Rehman Naseer ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Muslim League (PML-Q).[5]
An sake zaɓen shi a Majalissar Lardi ta Punjab a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar PP-114 (Gujrat-VII) a babban zaɓen Pakistan na shekarar ta 2013 .[6] Ya samu ƙuri'u 40,428 sannan ya doke Raja Muhammad Naeem Nawaz ɗan takarar Pakistan Tehreek-e-Insaf (PTI).[7]
Manazarta