Mohammed Magoro

Mohammed Magoro
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015 - Abdul-Aziz Nyako
District: Adamawa Central
Rayuwa
Haihuwa 7 Mayu 1941 (83 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Digiri Janar
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Mohammed Magoro (an haife shi aranar 7 ga watan Mayu a shekara ta 1941) shi ne Manjo Janar na sojan Najeriya da ya yi ritaya wanda ya taba yin ministan gwamnati sau biyu, a karkashin Janar Obasanjo da Buhari. A zaɓen watan Afrilun a shekara ta 2011 an zabe shi Sanata na mazabar Kebbi ta Kudu a Jihar Kebbi, Najeriya .

Farkon aiki

An haifi Magoro ne a jihar Kebbi, dan kabilar Zuru marassa rinjaye. Ya yi karatun digiri na biyu a makarantar lardin Bida, abokin karatun Mamman Jiya Vatsa da Ibrahim Babangida . Ya shiga aikin sojan Najeriya ne a ranar 10 ga Disamban shekarata 1962 tare da Ibrahim Babangida da Sani Abacha, lokacin da ya shiga Kwalejin Horar da Sojoji ta Najeriya.

Mulkin soja

An naɗa Magoro Kwamishinan Sufuri na Tarayya a lokacin mulkin Soja na Janar Olusegun Obasanjo a shekarar 1978. Ya zama Ministan Harkokin Cikin Gida a lokacin Manjo Janar Muhammadu Buhari, shugaban mulkin soja daga Janairu shekarar 1984 zuwa Agusta 1985. Ya kuma kasance memba na Majalisar Koli ta Soja. A matsayinsa na Ministan Harkokin Cikin Gida, a cikin Mayu 1985 ya lura da ƙaurar kusan 'yan ƙasashen waje miliyan daga Nijeriya. Rabin sun fito daga Ghana, sauran kuma daga wasu kasashen Afirka ta Yamma inda suke tserewa daga fari da yunwa.

Ba a ci gaba da rike Magoro a matsayin minista ba a karkashin Sabon mulkin Ibrahim Babangida wanda ya karbi mulki a watan Agusta na shekarar 1985, amma an nada shi shugaban Layin Lantarki na Najeriyar, da Hukumar Jiragen Kasa da Hukumar Kula da Tashar Jiragen Ruwa ta Najeriya . Bayan ya yi ritaya a 1995 ya koma aikin gwamnati sannan daga baya ya zama Shugaban Kamfanin Ltd.

Jamhuriya ta hudu

Magoro ya zama Shugaban ƙungiyar Oando a shekarar 2000, wani kamfanin tallata mai wanda aka kirkireshi ya hanyar sayar da kamfanin Unipetrol Nigery Plc., Inda kamfanin suka sayi babban kaso. A watan Nuwamba na 2001 Magoro ya kasance mamba a cikin Kwamitin Amintattu na Jam'iyyar PDP. Gabanin zaben watan Afrilun 2007 na gwamnan jihar Kebbi, da farko an bayyana Magoro a matsayin dan takarar PDP amma daga baya aka maye gurbinsa da Alhaji Saidu Dakingari . A lokacin da aka ci gaba da zaben Dakingari, jam’iyyun da ke hamayya da juna sun yi sabani kan sahihancin zaben bisa la’akari da cewa an gabatar da shi a matsayin dan takara a ranar 5 ga Fabrairu 2007 amma bai shiga jam’iyyar ba a hukumance har sai 10 ga Fabrairun shekarar 2007.

Aikin Sanata

A zaɓen fitar da gwani na PDP na watan Janairun shekarar 2011 a Zuru dan takarar Sanata na Kudancin Kebbi, Magoro ya kayar da mai ci, Sanata Tanko Ayuba . Mogoro ya lashe zaben a ranar 9 ga Afrilu 2011 tare da 125,940. Wanda ya zo na biyu shi ne Abubakar S. Yelwa na jam’iyyar (Congress for Progress Change (CPC) Wanda ya samu kuri'u 94,147.

C)



(CPC), wanda ya samu kuri’u 94,147.

Manazarta

1.Max Siollun (2009). Oil, politics and violence: Nigeria's military coup culture (1966-1976). 2.Algora Publishing. p. 144. ISBN 0-87586-708-1. 3. "NDA – Ministry of Defence". Retrieved 24 May 2020. 4."Major General Mohammed Magoro (RTD) PSC". Oando. Retrieved 6 May 2011. 5."PDP's Men of Power". ThisDay. 10 November 2011. Archived from the original on 2 December 2005. Retrieved 6 May 2011. 5. "Nigeria a Ragged Exodus of the Unwanted". Time Magazine. 20 May 1985. Retrieved 6 May 2011. 6. "Appeal Court confirms elections Governors Shinkafi of Zamfara and Shekarau of Kano valid". esinislam.com. 10 April 2008. Retrieved 6 May 2011.