Maureen Eke (an haife ta 19 ga watan Disamban 1986) 'yar wasan ƙwallon ƙafa ta mata ce ta duniya wacce ke buga wasan tsakiya.[1] Ta kasance memba a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya kuma tana cikin tawagar gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA 2007. A matakin kulob, Eke tana taka leda a kulob ɗin Delta Queens FC da ke Jihar Delta a Najeriya.
Manazarta
- ↑ List of Players" (PDF). FIFA Women's World Cup China 2007. FIFA. 2007. Archived from the original (PDF) on 14 October 2012. Retrieved 28 September 2007