Masarautar Patigi Jiha ce ta gargajiya ta Najeriya wacce Idrissu Gana na ɗaya ya kafa ta a shekarar 1898, sunan patigi yana nufin ' karamin tudu ' Masarautar dake cikin ƙaramar hukumar pategi ta jihar kwara kuma babban birnin Pategi.[1]
Masarautar
Idrssu Gana ne ya kafa Masarautar wanda a shekarar 1898, ya jagoranci wata ƙungiya (Kede), wata ƙungiya ce ta ƴan ƙabilar Nupe daga Bida a yakin da Turawan Mulkin Mallaka suka yi, kuma mutanen Nupe da yare na Yarbawa ne ke zaune a masarautar. daga cikin mutanen akwai manoma masu fatauci da masunta.[ana buƙatar hujja]
Masarautar duka mutanen Nupe ne a cikinta kuma tana gudanar da bikin kwale-kwale da aka fi sani da Bikin Pategi Regatta wanda aka yi akasari a yankin kogin Neja a bakin Tekun Patigi. Taron kwale-kwale na tarihi da kuma yawon buɗe ido da Farfesa Idrissu Aliyu ya ce majalisar gargajiya ta Masarautar ne suka kafa ta a shekarar 1949 a hannun shugaban majalissar guda biyu, Ahman Pategi da Etsu Umaru Bologi I, an fara gudanar da bikin-ne a shekarar 1952, bakin kogin Niger Kwara da Niger Kogi. Bikin wanda ya ƙunshi tseren kwale-kwale ko kwale-kwale ya haɗa da baje kolin a Nijar Gbaradogi da ke gabar kogin yamma, Masarautar kuma ta yi bikin ranar al'adun Nupe da ake gudanarwa duk shekara a watan Yuli kuma ya kasance tarihin mamaye yankin Nupe gaba ɗaya kan Turawan mulkin mallaka.[2][3]
Jerin masu mulki
Sunan sarki a pategi ana kiransa da Etsu na Patigi. Etsu na Patigi na yanzu shine Alhaji Umar Bologi II.[4][5] Jerin sarakunan gargajiya na masarautar Patigi da aka fi sani da Etsu Patigi da aka kafa a ƙarni na 16:[6][7]
Etsu Idrissu Gana ɗan Muazu Isa I (b. 1856 - d. 1900). 1898-1900
Muazu Isa dan Idrissu Gana (b. 1882 - d. 1923). Nuwamba 1900 - 1923
Usman Tsadi dan Muazu Isa (d. 1931) 1923 -January 1931
Umaru dan Muazu Isa (b. 1898 - d. 1949) Janairu 1931 - 1949
Umaru Ibrahim Bologi 1st term (b.1939 - 2018) 1949 - 1966
↑Jimada, Idris Sha'aba. (2016). The historical background to the establishment of Patigi Emirate : c. 1810-1898. ISBN978-978-54467-9-1. OCLC1122566972.