Masanin yanayin ƙasa masanin kimiyyar zahiri ne kuma masanin kimiyyar zamantakewar Dan Adam wanda yanke binciken sa akan labarin ko yanayin ƙasa, nazarin muhalli, nazarin zamantakewar ɗan Adam, gami da yadda al'umma da yanayi ke cuɗanya. Ma'anar kalmar "geo" ta Helenanci tana nufin "duniya/ƙasa" ita kuma kalmar Helenanci ta, "graphy," tana nufin "bayani," don haka geographer shine wanda ke nazarin duniya.[1] Kalmar “geography” kalma ce ta Tsakiyar Faransa wacce aka yi imanin cewa an fara amfani da ita a 1540.[2]
Duk da cewa anfi sanin masana yanayin kasa a tarihance da yin Nazarin taswira kadai, zana taswira na daga cikin ainihin fannin nazarin zane-zanen taswira, wani bangare na yanayin kasa. Masana ilimin kasa ba wai kawai suna nazarin yanayi ne ko zamantakewar ɗan adam kadai ba, suna nazarin dangantakar da ke tsakanin waɗannan biyun. Alal misali, suna nazarin yadda muhalli na zahiri ke ba da gudummawa ga zamantakewar ɗan adam da kuma yadda zamantakewar ɗan adam ke shafar muhalli. [3]
Musamman ma, masana ilimin kasa/yanayi na zahiri suna nazarin muhalli na zahiri yayin da masu binciken nazarin dan adam ke nazarin zamantakewa da al'adun ɗan adam. Wasu masanan kimiyyar ƙasa suna aiki ne a fanninGIS ( tsarin bayanan kimiyyar yanki geographic information system) kuma galibi ana amfani da su a hukummomin cikin gida, jihohi, da hukumomin gwamnatin tarayya da kuma a cikin kamfanoni masu zaman kansu ta kamfanonin muhalli da injiniyoyi.[4]
Hotunan da Johannes Vermeer ya yi mai taken The Geographer da The Astronomer duk ana tsammanin suna wakiltar tasirin bunkasa da kuma daukakar binciken kimiyya a Turai a lokacin da sukayi zane a shekarun1668-69.
Alexander von Humboldt (1769-1859) - ya wallafa Cosmos kuma tare da shi aka kirkiri fannin biogeography (wato nazarin tsirrai).
Arnold Henry Guyot (1807-1884) – lura da tsarin kankarar glaciers da ci-gaba fahimta a nazarin matsawar glacier, musamman hanzarin kwarara kankara.
Carl O. Sauer (1889-1975) – masanin ilimin kasa.
Carl Ritter (1779-1859) - ya mamaye kujerar shugaban farko na ilimin kasa a Jami'ar Berlin.
David Harvey (an haife shi a shekara ta 1935) - Mawallafin labarin kasa na Marxist kuma marubucin ka'idoji akan yanayin sararin samaniya da birane, wanda ya lashe kyautar Vautrin Lud .
Doreen Massey (1944-2016) – masani a sararin samaniya da wuraren dunkulewar duniya da jam’insa; wanda ya lashe kyautar Vautrin Lud.
Edward Soja (1940-2015) - yayi aiki akan ci gaban yanki, tsare-tsare da gudanar da mulki kuma ya sanya kalmomin synekism da postmetropolis; wanda ya lashe kyautar Vautrin Lud.
Ellen Churchill Semple (1863-1932) – shugabar mace ta farko ta Ƙungiyar Ma’aikatan Geographers ta Amurka .
Eratosthenes ( c. 276-c. 195/194 BC) – kirga girman Duniya.
Ernest Burgess (1886-1966) – mahalicci na concentric zone model .
Gerardus Mercator (1512-1594) - mai zanen zane wanda ya samar da tsinkayar Mercator
John Francon Williams (1854-1911) - marubucin The Geography of the Oceans .
Karl Butzer (1934-2016) – Masanin labarin kasa Ba-Amurke, masanin al'adu da kuma masanin ilimin kimiya na muhalli.
Michael Frank Goodchild (an haife shi a shekara ta 1944) - Masanin GIS kuma wanda ya lashe lambar yabo ta RGS a cikin 2003.
Muhammad al-Idrisi (Larabci: أبو عبد الله محمد الإدريسي; Latin: Dreses) (1100-1165) – marubucin Nuzhatul Mushtaq.
Nigel Thrift (an haife shi a shekara ta 1949) – mafarin ka'idar ba wakilci .
Paul Vidal de La Blache (1845-1918) - wanda ya kafa makarantar Faransanci na geopolitics, ya rubuta ka'idodin geography na ɗan adam.
Ptolemy (C. 100–C. 170) - an tattara ilimin Girkanci da na Roman a cikin littafin Geographia .
↑Arrowsmith, Aaron (1832). "Chapter II: The World". A Grammar of Modern Geography. King's College School. pp. 20–21. Archived from the original on 4 October 2021. Retrieved 4 October 2021.
↑"geography (n.)" (Web article). Online Etymology Dictionary. Douglas Harper. n.d. Archived from the original on 1 August 2017. Retrieved 10 October 2018.
↑Pedley, Mary Sponberg; Edney, Matthew H., eds. (2020). The History of Cartography, Volume 4: Cartography in the European Enlightenment. University of Chicago Press. pp. 557–558. ISBN 9780226339221. Archived from the original on 4 October 2021. Retrieved 4 October 2021.
↑"Geographers : Occupational Outlook Handbook : U.S. Bureau of Labor Statistics". www.bls.gov. Retrieved 6 October 2021.
↑Nel, Etienne (23 November 2010). "The dictionary of human geography, 5th edition - Edited by Derek Gregory, Ron Johnston, Geraldine Pratt, Michael J. Watts and Sarah Whatmore". New Zealand Geographer. 66 (3): 234–236. doi:10.1111/j.1745-7939.2010.01189_4.x. ISSN 0028-8144.
↑Marsh, William M. (2013). Physical geography : great systems and global environments. Martin M. Kaufman. Cambridge: Cambridge University Press. ISBN 978-0-521-76428-5. OCLC 797965742
↑"Geography Education @". Nationalgeographic.com. 24 October 2008. Archived from the original on 7 February 2010. Retrieved 16 July 2013.
↑Freeman, T. W.; James, Preston E.; Martin, Geoffrey J. (July 1980). "The Association of American Geographers: The First Seventy-Five Years 1904-1979". The Geographical Journal. 146 (2): 298. doi:10.2307/632894. ISSN 0016-7398. JSTOR 632894.
↑"AGS History". 26 February 2009. Archived from the original on 26 February 2009. Retrieved 11 October 2021.
↑"National Geographic Society". U.S. Department of State. Retrieved 11 October 2021.
↑"Royal Geographical Society - Royal Geographical Society (with IBG)". www.rgs.org. Retrieved 11 October 2021.
Kara karantawa.
Steven Seegel . Maza Taswira: Rayukan Juyin Juya Hali da Mutuwar Ma'aikatan Geographers a Ƙirƙirar Gabashin Tsakiyar Turai. Jami'ar Chicago Press, 2018. ISBN978-0-226-43849-8 .