Masallacin Omar Ibn Al-Khattab ( fassarar Spaniyanci Omar Iban Al-Jattab ) masallaci ne a Maicao, La Guajira, a Kasar Colombia. Shi ne masallaci na uku mafi girma a Latin Amurka. Ana kiran shi kuma da "La Mezquita" ("Masallacin"), saboda shine masallaci tak a yankin. Tare da Makarantar Dar Alarkan, su ne cibiyoyin addinin Musulunci da al'adunsu a yankin. An gina masallacin a ranar 17 ga watan Satumban 1997, kuma an sa masa suna bayan halifan Sunni na biyu Omar Ibn Al-Khattab .[1] Masanin gine-ginen na kasar Iran Ali Namazi ne ya zana masallacin, wanda injiniyan gine-gine Oswaldo Vizcaino Fontalvo ya gina, ta amfani da marmara ta Italiya don gina ta. Zai iya ɗaukar mutane aƙalla sama da mutum dubu ɗaya.
Cikin Masallacin
A bakin kofar akwai babban zaure wanda aka kawata shi da rubutun larabci. Bugu da kari, akwai wani zauren, wanda ya fi na farkon girma, inda maza ke sallah. Anan ne ma suke haduwa domin kawo karshen lokutan azumi. Soron wannan ɗakin yana da zane-zane na ado. Daga gabas akwai wurin da mata suke sallah, wanda ke sama da wurin ibada na maza. Saman masallacin zagaye yake da hasumiyoyi.
A kasan manyan matakalan fita daga masallacin akwai daƙin da ake yiwa mamaci wanka kafin a kai gawar zuwa makabartar Musulman yankin.
Duba kuma
- Jerin masallatai a Amurka
- Jerin masallatai
- Musulunci a Kolombiya
Manazarta
Hanyoyin haɗin waje