Maryam Musa Waziri

An haifi Maryam Musa Waziri a ranar 9 ga watan Nuwamba, shekara ta alif 1992 a Jihar Gombe, jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya. Ta girma a jihar Gombe kuma ta yi karatun firamare da sakandare. Jaruma Maryam Waziri ta yi digiri daga Jami'ar Maiduguri (UNIMAID).

Maryam Musa Waziri na daya daga cikin kyawawan jarumai a masana’antar fina -finan Hausa ta Kannywood. An fi saninta da Maryam Waziri. Maryam Waziri tayi Karatun firamare da na sakandare duk a jihar Gombe, inda aka haife ta.

Jaruma Maryam Waziri ta fito a fina -finan Hausa da dama, kuma a halin yanzu rahotonni sun nuna cewa tana daya daga cikin jarumai masu tsada a masana'antar fina-finanai ta Kannywood.

Maryam ta fito a fina -finai sama da 40 tun lokacin da ta samu kanta a matsayin Jaruma, Maryam Waziri ta fito a shirin fim inta na farko a shekarar 2015.[1]

Wasu daga cikin fina-finan ta

Yakin Mata, Yan Zamani, Amina Juna, Muguwar Mace, Yakin Mata, Labarina, da Dan Halak da dai sauran su.

Manazarta

Yakin Mata, Yan Zamani, Amina Juna, Muguwar Mace, Yakin Mata, Labarina, da Dan Halak

  1. https://www.haskenews.com.ng/2021/09/jaruma-maryam-musa-waziri-maryam-waziri.html?m=1