Martin Dominic Martin Hassan (an haife shi a ranar 16 ga watan Satumba Shekara ta 1999) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Sudan ta Kudu wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ulsan Citizen FC ta Koriya ta Kudu da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Sudan ta Kudu.
Aikin kulob
Sawi ya fara aikinsa a kulob din Young Stars na Sudan ta Kudu, [1] kafin ya koma Koriya ta Kudu a shekarar 2016 don shiga kulob ɗin Ansan Greeners. A cikin shekarar 2018, Sawi ya sanya hannu a kungiyar Goyang Citizen. [2] A cikin watan Janairu 2020, bayan ya zira kwallaye 19 a wasanni 35 na Goyang, Sawi ya sanya hannu a kulob din K3 League Yangju Citizen.[3]
Ayyukan kasa da kasa
A watan Nuwamba 2018, Sawi ya buga wasa a tawagar Sudan ta Kudu a 'yan kasa da shekaru 23 da Uganda a filin wasa na Juba. A ranar 17 ga Nuwamba, 2019, Sawi ya fara buga wa Sudan ta Kudu wasa a ci 2-1 da Burkina Faso.[4]
Manazarta
- ↑ "South Sudanese player signs to South Korean
Club" . Hot in Juba. Retrieved 12 December 2019.
- ↑ "[오피셜] 고양시민축구단, '남수단 네이마르' 마틴 영
입" (in Korean). Naver. 18 May 2018. Retrieved 26
March 2020.
- ↑ "Sawi Signs For A New Club in The South Korea
K3 League" . Kurra Sports. 7 January 2020.
Retrieved 26 March 2020.
- ↑ "South Sudan vs. Burkina Faso" . National Football
Teams. Retrieved 26 March 2020.