Malik Ibrar Ahmed ( Urdu: ملک ابرار احمد; an haife shi a ranar 3 ga watan Janairun 1970), ɗan siyasan Pakistan ne wanda ya kasance memba a Majalisar Dokokin Pakistan, daga shekarar 2008 zuwa watan Mayun 2018. A baya, ya kasance memba na Majalisar Lardi na Punjab daga shekarar 2002 zuwa ta 2007.
Rayuwar farko da ilimi
An haife shi a ranar 3 ga watan Janairun 1970 a Rawalpindi .[1] [2]
Ya sami digiri na farko na Arts daga Kwalejin Gwamnati Asghar Mall Rawalpindi a shekarar 1992.[2]
Harkokin siyasa
An zaɓe shi a Majalisar Lardi na Punjab a matsayin ɗan takarar Pakistan Muslim League (PML-N) daga Mazaɓar PP-10 (Rawalpindi-X) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2002 . Ya samu ƙuri'u 17,035 sannan ya doke ɗan takarar jam'iyyar Pakistan Peoples Party (PPP).[3]
An zaɓe shi a Majalisar Dokokin Pakistan a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar NA-54 (Rawalpindi-V) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2008 .[4][5] Ya samu ƙuri'u 58,228 sannan ya doke ɗan takarar jam'iyyar PPP. A wannan zaɓen, an sake zaɓar shi a matsayin ɗan majalisar dokokin jihar Punjab a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar PP-10 (Rawalpindi-X). Ya samu ƙuri'u 35,532 sannan ya doke Chaudhry Masood Akhtar ɗan takarar jam'iyyar PPP.[6] Ya bar kujerar majalisar Punjab.[7]
An sake zaɓen shi a Majalisar Dokoki ta Ƙasa a matsayin ɗan takarar PML-N daga Mazaɓar NA-54 (Rawalpindi-V) a babban zaɓen Pakistan na shekarar 2013 .[8][9][10][11] Ya samu ƙuri'u 76,336 ya kuma doke dan takarar Pakistan Tehreek-e-Insaf .[12]
Manazarta