The Washerman fim ne na wasan kwaikwayo na soyayya na Najeriya wanda akai a shekara ta dubu biyu da sha takwas 2018 wanda Etinosa Idemudia ya samar kuma Charles Uwagbai ya ba da umarni.[1] fim din Ik Ogbonna, Frank Donga, Mc Abbey, Bryan Okwara, Mofe Duncan, Judith Audu, Sound Sultan, Sexy Steel da Mercy Isoyip.[2]
Bayani game da fim
Labarin ya ta'allaka ne a kan wani vlogger wanda ke neman soyayya ta gaskiya. Tare da addu'o'insa, ya shawo kan damuwarsa kuma ya sami soyayya, kodayake ba abin da ake tsammani ba ne.[3]