Mai mala Buni, An haife shi 19 ga watan Nuwamba, shekara ta alif dari tara da sittin da bakwai 1967) Miladiyya.(A.c)Daya ne daga manya kuma jiga-jigan 'yan siyasar Najeriya. An haife shi a Buni Yadi dake karamar hukumar Gujiba, a Jihar Yobe, Najeriya. A halin yanzu shi ne zababben Gwamnan Jihar Yobe mai ci kuma shine shugaban riko na babban kwamatin riko kasa na jam'iyyar APC dake shugabancin Najeriya.[1][2]
Kafin zaben Gwamnan jihar Yobe, shine sakataren Jam'iyyar All Progressives Party (A.P.C) na kasa.
Siyasa
An zabi Mala Buni gwamna ne a babban zaben Najeriya na shekarar 2019 a watan Maris, karkashin jam'iyya mai mulki All Progressives Congress (APC).[3][4] gabanin zabensa gwamna,Buni shi ne Shugaban riko na jam'iyyar All Progressives Congress a yanzu bayan tsige tsohon shugaban jam'iyyar Adam Oshiomole.
Manazarta