Wacece mace An samu bayanai mabambamta da yawa game da wacece mace, inda masana da yawa sukai ta zubo baya nai kamar haka:
1. Falsafofin Girkawa suna rayawa cewa mace ba mutum bace, kawai Aljana ce
2. Hakama wani ɓangare na Larabawa shekaru masu yawa suna rayawa cewa mace kawai halittace kamar shauran dabbobi ko kayan abinci da Allah (S.W.A) Ya samar wa maza saboda haka namiji na da ikon mallakarta kamar yadda zai mallaki kaza ko shinkafa ko zomo a jeji, kuma na da ikon bautar da ita yadda yake so.
3. Haka nan ɓangaren Jamusawa sama da shekaru masu yawa suma suna ɗaukar mace a matsayin halitta sai dai bata da cikakken 'yanci da daraja kamar namiji.
4. Malaman kimiyya suma sun yadda mace mutunce kamar kowa sai dai yan canje canje na halayya da ɗabi'u da ba a rasa ba.
5. Duk a bayanai da aka yi a kan mace, ba a sami wani bayani wanda yaiwa mace adalci ba, irin bayanin da musulunci da malaman kiymiyya sukace akan mace.
Mace ba dabba bace ba kuma aljana ba ce, halittace wadda babu banbanci tsakanin namiji da mace a ɓangaren ɗan'adamtaka. Mace na da cikakken yanci da iko daidai da ita a musulunci, namiji ya zam mai mata hidima har tsawon rayuwarta ta hanyar ɗaukemata nauyinta da buƙatunta na rayuwa. Muslunci ya ba da umarni a girmama su, a nemi shawararsu. Wacece mace a mahanga ta masana soyayya?
Mace kishiyar jinsin da namiji ce wacce aka baibaye ta da abubuwan sha'awa, a wani mataki na rayuwarta. Mace na da wasu sinadarai na kwarjini ga ɗa namiji (driving force) wadda takan sarrafa ɗa namiji yadda take so.
Mace a fage na soyayya tana da rauni da tausayi da saurin amincewa da wuyar sha ani. Ƙarin bayani daga malaman kimiyya sunce mace nada rangwamen tunani a kan ɗa namiji sai dai sunfi namiji saurun haddace abu suna iya riƙe abu a kansu shekara da shekaru ,basu mantaba . Mata kan samun tawaya a tunanin su, rashin nutsuwa canji ajikinsu adukkan kowane wata yayin yin wata ibada tasu ta al'ada me mata suke so?
1. Kulawa
Ba abin da mata suka fi so irin nuna musu kulawa da damuwa ta hanyar nuna musu soyayya ɗaukar nauyinsu da kare musu buƙatunsu da dukiyarar da mutuncinsunsu.
2. Nishaɗi
mata na son nishaɗi mafiya yawan lokuta a rayuwarsu, dan haka abokina kazama me shiryawa iyalanka nishaɗi a kai akai dan sasu farin cikin.
3. Jarumtaka: Mata na son su ga mutum jarimi, imma na ƙarfi ko jarimtaka da ilmi da fasaha, suna alfahari da saurayi mai ƙarfi da ilimi da addini da fasaha da shauransu. Mata sun bawa Musulunci gudunmawa sosai da dukiyarsu da rayukansu da lokacinsu .