Look at the King in the Moon (Faransanci: Regarde le roi dans la lune) fim ne da aka shirya shi a shekarar 2011 wanda Nabyl Lahlou ya ba da umarni.[1][2][3][4] An nuna shi a bikin fina-finai na ƙasa da ƙasa na Alkahira.[5]
Takaitaccen bayani
‘Yan sanda sun azabtar da shi suna neman cire masa ikirari game da dangantakarsa da wani William Shakespeare, Fettah Aberkane ya faɗa cikin suma. A cikin raɗaɗin da ya ke yi, ya yi tunanin fim ɗin da ya yi mafarkin yin shi.[6]