Lola Ibrahim

Lola Ibrahim yar ra'ayin kare hakkin ɗan adam wanda a turance ake kira da "Activist". An haife ta a jahar Gusau dake arewa cin Nijeriya. Asalin iyayen ta yarbawa ne watau mutanen kudancin Nijeriya ne.[1]

Karatu

Lola Ibrahim tayi karatu na zanen gidaje wanda aka fi sani da turanci da "Architecture". Bayan karatun datayi na Zane-zane wanda har tasamu shaidar kungiyar ta ƙasa amma ta juya ta zama yar gwagwarmaya kare hakkin mutane a Nijeriya.

Ilimi

Tana da ilimin boko, kuma tana jin Hausa, Nupe, English da kuma Yoruba. Ta iya rubutu a dukkan wannan yarikan da aka lissafa.[2]

Gwagwarmaya

Ita ɗin tayi gwagwarmaya wurin kare rajin ɗan adam musamman mata don ganin a basu hakin matan aure da kuma yara maza da mata. Ta samu damar buɗe ƙugiya don kare hakkin ɗan adam mai suna "Wo-Men Against Violence and Exploitation" watau "W.A.V.E Foundation" don ɗabaƙa rayuwar mata daga dukkanin tashin hankali da suke fuskanta a Nijeriya.[1][3]

Manazarta