Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Nekede babbar kwaleji ce mallakar gwamnatin tarayya da ke Nekede, karamar hukumar Owerri Westa jihar Imo, Kudu maso Gabashin Najeriya. An kafa ta ne a wani wuri na wucin gadi a harabar Government Technical College ta Jihar Imo a shekarar 1978 a matsayin Kwalejin Fasaha, Owerri kafin a matsar da ita zuwa inda take a yanzu a Nekede. A ranar 7 ga watan Afrilu na shekarar 1993, aka canzawa polytechnic ɗin suna zuwa kwalejin fasaha ta tarayya kuma aka sauya masa suna zuwa "Federal Polytechnic, Nekede". A cikin Federal Polytechnic, Nekede a na bada horon karatu da shaidar National Diploma da Higher National Diploma.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.